[DOWNLOAD] "RUDUN JUYIN HALITTA" by Adnan Oktar " Book PDF Kindle ePub Free
eBook details
- Title: RUDUN JUYIN HALITTA
- Author : Adnan Oktar
- Release Date : January 02, 1991
- Genre: Science & Nature,Books,
- Pages : * pages
- Size : 1447 KB
Description
Ga wasu mutane, zatonsu ka’idar juyin halitta ko ‘Darwiniyanci’ yana dauke ne da wasu ma’anoni da suka shafi kimiyya ne kawai, suna ganin bashi da alaka ko wata dangantaka da rayuwarsu ta yau da kullum. Hakika wannan shine fahimta karkatacciya wadda tafi shahara. Ya zarce duk inda tunani ya kai akan cewa ya shafi kimiyya ne, sai dai ita ka’idar juyin halitta tana kunshe ne da dabaibayin mayaudaran falsafawa wadanda suka tafi da tunanin mutane da yawa : wato akan jari-hujja.
Fasafawan jari-hujja, wadanda suka yarda da samuwar tarin kwayoyin halitta, kuma suka fadi cewar wai mutum ya samo asali ne daga tarin wadannan kwayoyi, har ma suka shelanta cewa, mutum ba komai bane illa dabba, tare da rikicin da shine sanadiyyar samuwarsa. Koda yake sun yada cewar wata hanyar ilmantarwa ce ta zamani akan falsafar kimiyya, alhali jari-hujja ne. Fahimtar Girkawan Da, da imaninsu akai shine yasa aka samu maguzawan falsafawan karni na goma sha takwas, suka farfado da ita kuma suka raya ta. Daga baya aka sake dasa ta a cikin karni na goma sha tara, ta bangarorin kimiyya daga wasu masu bautar tunani, kamarsu Karl Marx, Charles Darwin da Sigmund Freud.
Gano asalin wannan falsafar, wadda take da tambayoyi da yawa da zata amsa dangane da annobar da dan Adam ya jawo a karni biyun da suka wuce, za’a iya gani a cikin kowace akida da fahimta a cikin al’umomi, a matsayin dalili ne ga rikici ko sabani.
Ka’idar juyin halitta, ko Darwiniyanci, yazo ne don ya cike gurbin almara. Ya bayyanar da cewa jari-hujja wata fahimta ce a kimiyya. Shine yasa Karl Marx Uban kwaminisanci da Tsantsar jari-hujja, ya rubuta cewar Darwiniyanci shine « asali mai tabbaccen tarihi » akan ra ‘ayoyinsa a duniyance.
Babu shakka, wannan asali rubabbe ne. Domin bincike na kimiyyar zamani ya tabbatar Lokaci bayan Lokaci cewar shahararriyar yarda dake da alaka da Darwniyanci da kimiyya karya ce. Kuma hujjoji na kimiyya sunci karo da Darwiniyanci bayyana cewa Asalin halittarmu ba wai juyin halitta bane, sai dai Ubangiji shine ya halicci duniya, dukkan wani abu mai rai da kuma mutum.
An rubuta wannan littafi ne don a tabbatarwa da mutane akan haka. Tun lokacin da aka rubuta shi, asalinsa a harshen kasar Turkey, sannan a kasashe da dama, miliyoyin mutane sun karanta kuma sun gamsu da littafin. Kari akan harshen Turkawa, an fassara shi da Turanci, Italiyanci, Sifananci, Bosniyanci, Larabci, harshen Mayal da Indonesia. Wannan littafi yana nan a wadace, kuma kyauta a kowane harshe da aka ambata a hanyar sadarwa ta internet (www.evolutiondeceit.com)
Fatanmu ne ace Rudun Juyin Halitta ya dade yana bada gudunmawarsa ta wayar da kai akan rudun da Charles Darwin ya kawo wanda ya dade yana batar da mutane tun daga karni na 19. Kuma ya tunasar da mutane akan gaskiyar al’amarin rayuwarsu, kamar yadda suka zo duniya (ma’ana halittarsu) da kuma nauyin da yake kansu a wajen bautar Ubangijinmu.
Tarihin Marubuci
Marubucin, wanda yake rubutu a karkashin sunan alkalami HARUN YAHYA, an haife shi a shekara ta 1956.Bayan ya kammala karatunsa na firamare da sakandire a Ankara, sai ya tafi Jami`ar Mimar Sinan a Istanbul yayi digirinsa, sannan ya sake yin wani a fannin falsafa a jami`ar Istanbul.Tun daga 1980, marubucin ya wallafa littattafai akan siyasa, da wadanda suka shafi imani da kuma sha`anin kimiyya. Harun Yahya sanannen marubuci ne wanda ya rubuta muhimman ayyuka dake bayanin yaudarar ma`abota (evolution) juyin halitta, rashin gaskiyar da`awarsu da kuma bakar alaka dake tsakanin Darwin da munanan akidunsa.
Sunansa na alkalami ya kunshi sunaye guda biyu Harun da Yahya, don tunawa da wadannan manyan annabawa, wadanda suka yaki kafirci. Hatimin manzon Allah dake bangon littattafan marubucin yana da ma`ana da take da alaka izuwa abinda yake ciki. Hatimin kansa yana wakiltar Alkur`ani ne a matsayin littafin karshe wanda Allah ya saukar kuma kalmomin karshe